Wasanni: Karanta jiga-jigan yan wasa 6 da ke shirin barin kungiyar Real Madrid

Wasanni: Karanta jiga-jigan yan wasa 6 da ke shirin barin kungiyar Real Madrid

- Real Madrid ta yi fice wajen sayen 'yan wasan kwallon kafa mafiya tsada a duniya, sai dai wannan karon ita ce za ta karbi makudan kudin da ake zawarcin 'yan wasanta.

- Watakila 'yan kwallon Real Madrid shida ne ake sa ran za su sauya sheka da zarar an bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafa ta bana.

Cikin 'yan kwallon da ake hasashen za su bar Santiago Bernabeu sun hada da Fabio Coentraro da Pepe da James Rodriguez da Alvaro Morata da Diego Llorente da kuma Mariano Diaz.

Legit.ng ta samu labarin cewa shi Coentraro ana rade-radin Sporting Lisborn zai koma taka-leda aro, Pepe kuwa yarjejeniyarsa ce za ta kare a karshen watan Yuni, kuma kila Paris zai koma buga tamaula.

Wasanni: Karanta jiga-jigan yan wasa 6 da ke shirin barin kungiyar Real Madrid
Wasanni: Karanta jiga-jigan yan wasa 6 da ke shirin barin kungiyar Real Madrid

Sauran 'yan wasa hudun da suka rage a nan ne Real Madrid za ta karbi kudin da ake cewa zai kai Yuro miliyan 160.

Madrid ba ta son sayar da Morata wanda Manchester United ke zawarci kan kudi kasa da Yuro miliyon 90, haka kuma kungiyar na sa ran samun Yuro miliyan 70 kudin James Rodriquez.

Real Sociedad na zawarcin Llorente kan Yuro miliyan 8, shi kuwa Mariano Diaz zai iya barin Barnabeu kan Yuro miliyan 5.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel