Rashin Imani: Wata mata a kotu sakamakon cinnawa ‘yar riko wuta saboda zargin sata

Rashin Imani: Wata mata a kotu sakamakon cinnawa ‘yar riko wuta saboda zargin sata

An gurfanar da wata mata Uzoma Austin mai shekaru 34 a gaban kotun majistare da ke jahar Lagos a bisa laifin cinnawa wata ‘ya da ta ke riko wuta, lamarin da ya sa yarinyar ta samu muggan ciwukan kuna.

Abun ya faru ne a ranar 8 ga watan nan a yayin da matar ta zargi yarinyar wacce shekarun ta 12 kacal da laifin sace mata naira 1000, kamar yadda dan sandan da ya shigar da kara, sajant Lucky Ihiehie, ya fadawa kotun.

Laifin ya sabawa sashe na 242 da 243 na kundin dokar jahar Lagos, wanda ya tanadar da hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 14 da shekaru 7 ga laifukan biyu.

Sai dai matar ba ta amsa laifukan na ta ba.

Rashin Imani: Wata mata a kotu sakamakon cinnawa ‘yar riko wuta saboda zargin sata
Rashin Imani: Wata mata a kotu sakamakon cinnawa ‘yar riko wuta saboda zargin sata

Legit.ng ta samu labarin cewa da farko an kwantar yarinyar asibitin koyar wa na jahar Lagos LASUTH, wanda daga bisani aka mika ta ga asibitin Gbagada inda anan ne take samun kulawa yanzu.

Alkalin kotun Misis Sule Amzat ta bayar da belin matar akan Naira 50,000, da mutane biyu da za su tsaya mata.

An daga sauraran karar zuwa ranar 8 ga watan Yuli.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel