Karyar banza ce; Ina nan a APC Inji Honarabul Abdulmumin Jibrin

Karyar banza ce; Ina nan a APC Inji Honarabul Abdulmumin Jibrin

– Dan Majalisar Kano Abdulmumin Jibrin ya karyata rade-radi

– ‘Yan Jarida sun rahoto cewa an salami Dan Majalisar daga Jam’iyyar APC

– Honarabul yace aikin makiya ne kurum wannan magana

Dan Majalisa Abdulmumin Jibrin yace yana nan a Jam’iyyar APC. Honarabul Jibrin yace yana da alaka mai kyau da Jam’iyyar mai mulki. Ko da dai yanzu haka Majalisar Wakilai ta dakatar da shi tun bara.

Honarabul Abdulmumin Jibrin
Ina nan a APC har gobe-Jibrin

Dazu kun ji cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta sallami Dan Majalisar nan da aka dakatar a dalilin wasu laifuffuka da yayi mata. Hon. Abdulmumin Jibrin din yayi wuf ya karyata wannan maganar inda yace sharrin makiya ne a shafin sa na Tuwita.

KU KARANTA: A je ayi katin zama Dan Jiha Inji Gwamnan Kaduna

Karyar banza ce; Ina nan a APC Inji Honarabul Abdulmumin Jibrin
Honarabul Abdulmumin Jibrin a mazabar sa kwanan nan

Jibrin mai wakiltar Kiru da Bebeji yace yana da alaka mai kyau da Jam’iyyar kuma wannan labarin ba daga Jam’iyyar ya fito ba. NAIJ Hausa dai tayi kokarin tuntubar sa a waya amma bai dauka ba.

Dan Majalisar dai kwanan nan ma ya rabawa mutanen mazabar sa kayan azumi masu yawan gaske inda har Gwamnan Jihar ya halarci taron. An dakatar da shi a Majalisa bayan zargi shugabannin ta da zargin cushe a kasafin kudi bara.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Nnamdi Kanu ya shirya balle Jama'a daga Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel