Dakarun Soji sun kakkaɓe ɓarayin shanu daga dajin jihar Kaduna
- An kama ƙasurgumin dan fashi mai garkuwa da mutane a Kaduna
- Dakarun Sojin runduna ta daya da gudanar da wani aiki na musamman
Sakamakon sake farfadowar ayyukan miyagun mutane masu garkuwa da mutane a kan titin Kaduna zuwa Abuja, dakarun Sojin runduna ta daya da gudanar da wani aiki na musamman don magance matsalar.
Cikin wata sanarwa da Kaakakin rundunar Soji, Birgediya SK Usman ya fitar, ya bayyana cewar dakarun Sojin sun kai samame ne a dajin garin Rijana a ranar Laraba 14 ga watan Yuni na shekarar 2017.
KU KARANTA: Mutane 6 sun mutu, 20 sun jikkata a yayin gobarar bene mai hawa 27 (Hotuna)
Sojojin sun dira dajin ne, wanda yayi kaurin suna wajen kasancewa mafakar yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane, inda suka samu nasarar cafke wani kasurgumin dan fashi da suka dade suna dakonsa.
Legit.ng ta samu rahoton sunan wannan dan fashi Sani Ibrahim, amma an fi saninsa da suna Burtu, sa’annan sojojin sun gano babur guda 1 da akuyoyi 25 duk a dajin.
Haka zalika, Sojojin sun kai wani samame a kan iyakar jihar Kebbi da Zamfara, inda suka kashe yan fashi guda 3, tare da kwato shanu 134 da tinkiya 13.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Shekaruna 21 lokacin dana shiga yakin Biyafara
Asali: Legit.ng