Sojojin saman Najeriya sun yi abin yabawa

Sojojin saman Najeriya sun yi abin yabawa

– Rundunar Sojin saman Najeriya sun yi abin-a-yaba masu

– Sojojin Najeriya sun gyara injin wani babban jirgin sama

– Ba shakka dai ana samun cigaba wajen harkar tsaro a kasar

Sojojin Najeriya sun gyara injin wani babban jirgin yakin Alpha Jet. Rundunar Sojin Kasar da ke Garin Kayinji su ka yi wannan kokari. Kwanan nan aka koyawa wasu Sojojin aikin gyaran jirgin saman na Alpha Jet.

Sojojin saman Najeriya sun yi abin yabawa
Shugaban Hafsun Sojojin saman Najeriya da rundunar sa

Rundunar Sojin saman Najeriya sun yi abin burgewa inda su ka yi daya-daya da wasu manyan jiragen yaki na Alpha jet har guda 6. Da farko dai wasu Turawa da za a dauko su yi wannan aikin sun nemi a biya su kudi har Dala Miliyan 2.4.

KU KARANTA: A gina kurkuku a Dajin Sambisa Inji Sambisa

Sojojin saman Najeriya sun yi abin yabawa
Air Marshal Sadique Abubakar a tashar Sojin sama da ke Kayinji

Kanikawan Sojojin sama na kasar da ke tashar Kayinji a Jihar Neja ne dai su kayi wannan kokari. Dama can an koyawa wasu daga cikin Sojojin Najeriyar aikin gyaran a Kasar Kanada wajen wani horo da aka ba Sojojin.

Ana dai ganin canji tun bayan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sababbin hafsun Sojojin kasar inda Air Marshal Sadique Abubakar ke rike da Sojojin sama. Jiya kuma kun ji cewa Hukumar NDLEA ta damke wani Jami’in ‘Dan Sanda manyan buhuna har kusan 50 na wiwi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Da gaske 'Dan Sanda abokin kowa ne kuwa?

Asali: Legit.ng

Online view pixel