Rundunar ‘Yan sanda za suyi atisayi a Abuja

Rundunar ‘Yan sanda za suyi atisayi a Abuja

- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewa za su yi atisayi a Abuja a ranar Asabar mai zuwa

- Ta bukaci karda mutanen yankin su tayar da hankulan su a kan haka

Rundunar ‘yan sanda a Abuja, ta bayyana cewa, za su yi atisayi a Abuja a ranar Asabar 17 ga watan Yuni.

Sai dai sanarwar da suka fitar ta ce kada kowa ya firgita, domin atisayi ne za su yi saboda kara gwada karfi da dabarun kwantar da tarzoma.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan Majalisa sun karawa kan su kudi cikin kasafin kudin 2017

Rundunar ‘Yan sanda za suyi atisayi a Abuja
Rundunar ‘Yan sanda za suyi atisayi a Abuja

Har ila yau sun shawarci al’umma musamman mazauna yankunan Nyanya, Karshi da kuma Jikwoyi da su kwantar da hankulan su saboda su ne rugugin wutar zai fi damu, saboda su ne suka fi kusa da filin da ‘yan sandan ke yin atisaye.

Sanarwar da kakakin yada labaran ‘yan sanda na kasa ya bayar, ya ce za a gudanar da atisayen ne tun daga karfe 7 na safe har zuwa 4 na yamma.

Mista Omorodion ya kuma ja kunnen mazauna wadancan yankuna da ya ambata a baya da su kaurace wa kusantar wurin da za a gudanar da atisayen a tsawon lokutan da ya bayyana.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Legit.ng ta kawo maku bidiyon hira da tayi da jama'a na ko sun dauki rundunar 'yan sandan Najeriya a matsayin abokai

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng