Paparoma ya yi barazanar dakatar da wasu limaman Najeriya
- Paparomaya bai wa wasu limaman majami'u, a yankin kudu maso yammacin Najeriya, wa'adin wata daya don suyi biyayya ga Bishop da fadarsa ta nada
- Ya yi barazanar ne a gurin wata ganawa da ya yi da tawagar cocin na jihar Imo
- Wasu mabiya darikar Katolika sun nuna turjiya gurin yi ma zabin Paparoma biyayya saboda ba dan garinsu bane
Paparoma Francis na darikar Katolika ya bai wa wasu limaman majami'u, a yankin kudu maso yammacin Najeriya, wa'adin wata daya, ko ya dakatar da su, idan ba su yi biyayya ga Bishop din da fadarsa ta nada ba.
A cewar rahotanni, Paparoman ya yi barazanar ne a ganawar da ya yi da wata tawaga daga cocin na gundumar Ahiara da ke jihar Imo.
Wasu mabiya darikar Katolika a yankin ne ke nuna taurin kai gurin yin biyayya ga nadin da Paparoma Benedict ya yi wa Peter Okapaleke a matsayin Bishop din gundumar a shekarar 2012.
Rahotanni sun ce wasu limaman cocin ba sa yi masa biyayya ne saboda shi ba dan garin ba ne.
KU KARANTA KUMA: Hukumar DSS ta damke masu garkuwa da mutanen da suka addabi jama’a
Jaridar Vatican L'Osservatore Romano ta ba da rahoton cewar Paparoma Francis ya dauki matakin ne da manufar yin abin da ya dace ga bayin Allah.
Hakan ya hada da yin barzanar dakatar da limaman idan ba su rubuta wasikar cikakkiyar biyayya da kuma yarda da nadin Bishop Okpaleke ba zuwa ranar 9 ga watan Yuli.
Akwai mabiya darikar Katolika da dama a Najeriya, kuma limaman cocin kan samu manyan mukamai daga fadar Vatican.
Legit.ng ta kawo maku bidiyo kan hadda al'umma ke rayuwa a Ohuhu dake jihar Abia
Asali: Legit.ng