Dan majalisar wakilai Honarabul Sani Danlami ya tallafa wa mutane 700 daga mazabarsa Katsina ta tsakiya (Hotuna)

Dan majalisar wakilai Honarabul Sani Danlami ya tallafa wa mutane 700 daga mazabarsa Katsina ta tsakiya (Hotuna)

- Honarabul Sani Danlami ya tallafa wa mutane 700 daga mazabarsa Katsina ta tsakiya da babura, kekunan dinki

- Dan majalisar ya ce tallafin zai karade lungu da sakon mazabarsa

- Gwamna jihar Katsina Bello Masari ya yaba da wakilcin Mai Raba Alheri da yunkurinsa na tallafawa matasa da mata

A kokarinsa na kawo cigaba ga al'ummar da yake wakilta a zauren majalisar wakilai ta kasa, Sani Aliyu Danlami ya tallafawa mutane sama da 700 wadanda suka fito daga mazabarsa ta Katsina ta tsakiya, da babura, kekunan dinki ga mata da bada tallafin kudi 30,000 ga masu kananan da matsakaitan masana'antu.

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da bada tallafin wanda ya gudana a ofishinsa dake kan titin WTC dake cikin garin Katsina, Dan Majalisar Sani Aliyu (Mai Raba Alheri) ya ce: "wannan tallafi zai karade lungu da sakon mazabarsa.”

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, dan majalisar ya kara da cewa: "akwai motoci guda 2 wanda za a damkawa shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Katsina da kuma na Mazaba ta, watau wakilin Kudu 111. Har ila yau akwai mashina 160, wanda za a raba tsakanin matasa da kuma shugabanni na jam'iyya. Akwai kekunan dinki guda 100 da za a raba ga mata, wadanda sai da muka ba su horo na musamman a makaranta koyan sana'o'i dake nan Katsina domin koyan sana’a su za mo masu dogaro da kansu."

Dan majalisar wakilai Honarabul Sani Danlami ya tallafa wa mutane 700 daga mazabarsa Katsina ta tsakiya (Hotuna)
Gwamna Aminu Bello Masari na rabawa mata kekunan dinki guda 100

Dan majalisar wakilai Honarabul Sani Danlami ya tallafa wa mutane 700 daga mazabarsa Katsina ta tsakiya (Hotuna)
Dan majalisar wakilai Honarabul Sani Danlami na damkawa shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Katsina mabudin mota

Dan majalisar wakilai Honarabul Sani Danlami ya tallafa wa mutane 700 daga mazabarsa Katsina ta tsakiya (Hotuna)
Mashina 160 da za a rabawa matasa

Dan majalisar wakilai Honarabul Sani Danlami ya tallafa wa mutane 700 daga mazabarsa Katsina ta tsakiya (Hotuna)
Gwamna jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari da Dan majalisar wakilai Honarabul Sani Danlami da wasu jami'an gwamnati

Haka kuma akwai kudade da aka raba domin ga Exco kuma su 316 suka amfana da 30,000 ga kowanensu. Cikin Shugabannin Jamiyya akwai dari biyu da sittin da hudu; sauran kuma masu kada kuria ne. Akwai kuma mutane masu bukata ta musamman inda muka ba su 10,000 kowanensu ga mutum 100 da muka zakulo. Akwai kuma wadanda aka ba 5,000 su ma suna da dama.

KU KARANTA: Kujerar Sanata Melaye na rawa; yace Gwamnan Jihar Kogi ke kokarin ganin bayan sa

Ana shi jawabi gwamnan Jahar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana jin dadinsa bisa ga wannan tallafi inda ya nuna ba karamin alheri ba ne, duk ba kowa zai samu ba, saboda da zarar ana bayarwa to wata rana zai zo kanka. “Wadanda suka samu a cikinku don Allah ku yi amfani da shi hanyar da ya dace.” Inji gwamnan

Gwamnan ya kara da cewa a madadin abokan aikinmu matasa da iyayenmu mata muna mika godiya, Saboda mun gani a kasa kuma ina kira ga sauran da su yi koyi da abinda ka yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda mai martaba sarki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng