Uwa ta rikice: Diyar ta na soyayya da tsohon Mijin ta

Uwa ta rikice: Diyar ta na soyayya da tsohon Mijin ta

– Wata yarinya ta kama soyayya da Mijin Mahaifiyar ta

– Sai daga baya Mahaifiyar wannan yarinya ta gano haka

– Wannan yarinya tayi shekaru 20 tana kiran wannan mutumi ‘Baba’

Wani abin assha ya faru a can kasar waje

Wata Yarinya ce ta koma son mai gidan uwar ta

Jaridar Daily Mail ta rahoto wannan labari

Uwa ta rikice: Diyar ta na soyayya da tsohon Mijin ta
Budurwa ta auri mutumin da ta ke kira ‘Baba’

Mun samu labari daga Jaridar Daily Mail cewa wata mata ta rikice yayin da Diyar cikin ta ta buge da auren tsohon Mijin ta. Wannan yarinya dai ta zauna a matsayin agola a gidan wannan mutumi na fiye da shekaru 20.

KU KARANTA: Budurwa ta rasu bayan ta gama maganar mutuwa

Wannan abu dai ya ba matar mamaki yayin da Bazawarin na ta ya aure Diyar da ta haifa a waje kafin ta aure sa. Ta dai shigo gidan ne da wannan yarinya lokacin tana shekara 11 a Duniya. Matar tace sam wannan abu bai mata dadin ji ba.

Haka kuma rahotanni daga Kasar Sifen na nuna cewa babban Dan wasan nan na Real Madrid Cristiano Ronaldo ya samu jarirai tagwaye masu suna Mateo da Eve. Ko da yake dai har yanzu Dan wasan bai tabbatar da wannan abin farin cikin ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ta'aziya: Allah Sarki; An yi rashin Moji Olaiya [Bidiyo]

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng