An samu karuwa: Dan wasa Ronaldo ya samu ‘yan biyu
– Babban Dan wasa Cristiano Ronaldo ya samu karuwa
– An haifawa Ronaldo tagawayen ‘yan biyu
– Sai dai ba a san mahaifiyar jariran ba
Dan wasan Ronaldo ya samu tagwaye daga wata mata
Har yanzu dan wasan bai ce komai ba game da maganar
Kuma dai kun ji ba a san mahaifiyar ‘ya ‘yan ba
Rahotanni daga Kasar Sifen na nuna cewa babban Dan wasan nan na Real Madrid Cristiano Ronaldo ya samu jarirai tagwaye masu suna Mateo da Eve. Ko da yake dai har yanzu Dan wasan bai tabbatar da wannan abin farin cikin ba.
KU KARANTA: Ka ji abin da Messi ya fada game da Ronaldo
Kamar dai ‘Dan san a farko wanda ke da shekaru 6 a Duniya ba a san wanda ta haifi ‘ya ‘yan ba. Wata ce dai kurum aka ba aikin haifawa babban ‘Dan wasan ‘ya ‘ya domin kuwa iya sanin mu kawo yanzu budurwar sa ba ta da juna biyu
Kun ji dazu cewa Dan wasa Ronaldo ya samu jinjina daga Lionel Messi na Barcelona. Lionel Messi yace ba shakka Ronaldo babban Dan wasa ne. Idan kwallon kafa ake magana babu irin ‘Yan wasan biyu a Duniya.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ya za ayi idan mata ta fi miji albashi
Asali: Legit.ng