Adamawa: Kotu ta ci tarar gidan radiyo da telibijan Gotel mallakar Atiku Abubakar

Adamawa: Kotu ta ci tarar gidan radiyo da telibijan Gotel mallakar Atiku Abubakar

- Babban kotun jihar Adamawa ta ci tarar gidan radiyo da telibijan Gotel da ke Yola birnin jihar

- Wani dan jarida Kabiru Arayu ya shigar da kara yana neman a biyashi hakinsa

- Wannan shari'ar ta dau tsawon sama da shekaru 5 kafin yanke hukunci

- Kotun ta umurni gidan rediyon da telibijin ta biya dan jarida Kabiru Arayu diyyar naira miljyan 6.1 na karar da ya shigar

Bayan an kwashe shekaru 6 da Kabiru Arayu ya shigar da kara yana neman gidan rediyo da telibijan Gotel mallakar tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar a biyashi hakinsa, a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni kotu ta yanke hukunci inda ta tabbatar masa da abun da ya nema.

Babban kotun jihar Adamawa ta yanke hukumcin gidan radiyo da talabijan na Gotel da ke Yola fadar jihar, ya biya tsohon ma'aikacinsa dan jarida Kabiru Arayu diyyar naira miljyan 6.1 na karar da ya shigar na ci-da-guminsa.

Da ta ke yanke hukunci, mai shari'a Helen Nuhu Hammanjoda ta ce kotu ta dauki wannan matsayin saboda kin biyan dan jaridan hakkinsa na aikin kwangilar da yayi, kotu ta ce ya sabawa sashi na 167 karamin sashi na daya na dokar kasa.

Kotu ta ci tarar gidan radiyo da telibijan Gotel mallakar Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar mai gidan rediyo da telibijan Gotel da ke Yola

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, wannan hukunci na kotu na zuwa a lokacin da kungiyar 'yan jarida ta Najeriya ke kokawa da ci-da-gumin 'ya'yanta inda kafofin yada labarai da jaridu ke daukan 'yan jarida ba tare da biyansu albashi ko alawus-alawus ba.

KU KARANTA: Tattalin arziki: Najeriya ta hau tudun-mun-tsira Inji Dangote

Yayin da lauya mai kare dan jaridan Barrister Francis Ngaro ke sambarka da yadda shari'ar ta kaya, lauya mai kare gidan radiyo da telabijan na Gotel Ibrahim Gwary ya ce suna duba yiwuwar daukaka karar.

Tun farko, dan jarida Kabiru Arayu ya shigar da kara yana neman diyyar naira miliyan 20 da tara kamin hukunci da kotu ta bayar na a biya shi naira 6.1 a shari'ar da ta dau tsawon sama da shekaru 5.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Cikakken bayanin mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo kan yakin basasan Najeriya a cikin wannan bidiyon

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng