Abin dariya kuma abin tausayi, yadda wani dan bas da fasinja suka daku da juna har cikin lambatu (Hotuna)
- Fada ta kaure tsakani wani dan bas da fasinjan da ke cikin motan kan canji
- Mutanen biyu sun fafata har suka sami kansu cikin lambatu
- Sauran fasinjojin motar basu dakatar da fadan ba
Wani dan bas da fasinja suna takaman nuna gwaninta tsakanin su kamar yadda suka fafata da juna a kan kudi a bainar jama'a a Legas. Da alama cewa sararin da suke fadan bai ishe su ba sai kawai suka tutsar cikin wani lambatu a gaban fasinjojin jikin motar da kuma masu wucewa.
Legit.ng ta ruwaito cewa abin dariya a nan shine sauran fasinjoji wadanda ke kallon yadda fadan zai kasance sun ki dakatar da mutanen biyu kamar yadda suka ci gaba da fafatawa har cikin lambatu har suka samu gajiya.
KU KARANTA: Bayan El-Rufa’I ya alanta umurnin damke su, kungiyar matasan arewa sun shiga ganawa
Fafatawa tsakanin ‘yan bas dai da kuma fasinjoji a Legas ba sabuwar abu ba ce, abu ne dake faruwa yau da kulum. Abin mamaki a nan shine gaddama a kan kudi naira biyar kacal zai iya kai ku dare idan aka din ta faru tsakanin ku, don ba zasu taba yafewa ba, zai de kai ka bar musu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Na rasa yara 4 a cikin rushe-rushen gidajen mu da gwamnatin jihar Legas ta yi, a cewar wata mata a cikin wannan bidiyo
Asali: Legit.ng