Hattara! Kunji yadda ake safarar mutanen arewa zuwa kasashen waje?
Safarar mutane ya dauki wani sabon salo a arewacin Najeriya inda kamfanoni ke shiryawa mutane zuwa kasashe kamar Saudiya domin su yi aiki a gidajen Larabawa da zummar fita daga kuncin rayuwa da suke fama da ita a Najeriya.
Joli Oka Donli daraktar hukumar hana safarar mutane ta Najeriya tace ta samu labarin kamfanoni na safarar mutane zuwa Saudiya da wasu kasashen Larabawa kuma tace ta tura rahoton wa bangaren dake sa ido da binciken lamarin.
Legit.ng ta samu labarin cewa inji Joli Donli ana gudanar da bincike akan batun saboda haka tace ba zata yi magana a kai ba sai an kammala binciken. Amma ta jawo hankalin jama'a cewa su a hukumance basu ba kowa iznin yayi safarar 'ya'yan mutane zuwa kowace kasa ko kasashen Larabawa ba.
Wani likitan asibiti dake Abuja da suke tantance lafiyar wadanda ake safarar zuwa kasashen Larabawa yace abun akwai ban tsoro. Yace ana kawo yaran cikin motoci cike makil, maza da mata. Yanzu ma kusan gaba daya mata ake debowa a kawosu domin tantance lafiyarsu.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng