Zul waja haini: Yaro mai fuska 2 ya cika shekaru 13 (Hotuna)

Zul waja haini: Yaro mai fuska 2 ya cika shekaru 13 (Hotuna)

- An haifi wani yaro a kasar Amurka, can jihar Missouri mai fuskoki guda biyu,

- Yaron ya kwashe shekaru 13 yana rayuwa, ba kamar yadda likitoci suka ce zai mutu ba

Kimanin shekaru goma sha uku da suka gabata kenan aka haifi wani yaro a kasar Amurka, can jihar Missouri mai fuskoki guda biyu, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Masana sun bayyana cewar hakan na faruwa idan aka samu matsala a sinadarin Protein yayin halittar kokon kan mutum, kuma sun ce mutum 36 ne ke da irin wannan halittar a duniya gabaki daya, ind akawai wagegen gibi a bakin yaron, hanci biyu, katoton kai da kuma idanunsa sun yi nisa da juna duk a fuskar yaron.

KU KARANTA: Hukumar Sojin ƙasa zata gina jami’ar Sojoji a garin Biu

Iyayen yaron mai suna Tres Johnson, Brandy da Joshua sun yi ta fadi tashi don ganin sun ceto rayuwar yaron nasu, yayin da likitoci suka cika da mamakin yadda yaron yayi tsawon rai haka, alhali ire irensa na mutuwa ne tun suna jarirai.

Mahaifiyar yaron, Brandy tace “Bamu san mai zai faru da Tres ba anan gaba, babu wanda ya taba tunanin zai kawo yau, nayi farin cikin ganin wannan zagayoyar ranar haihuwarsa, shekaru goma sha uku a halin dayake ciki ba wasa bane.

“An sha fada mana ba zai rayu ba, har bana kirgawa, amma ga shi a yau ya kai 13, babu ilimi sosai akan irin halittarsu, sai dai wasu su kanzo da hanci 2, baki 2, idanu 4 da ire irensu, kuma suna mutuwa a jarirai, amma na Tres sai yazo da sauki, daban dana sauran." Inji ta.

Zul waja haini: Yaro mai fuska 2 ya cika shekaru 13 (Hotuna)
Tres: Yaro mai fuskoki 2 tare da yan'uwansa

Mjiyar Legit.ng ta cigaba da fadin “Akwai jinkiri a girman sa na yin hankali, don har yanzu tunanin jarirai ke gare shi, amma kuma ana samun cigaba, an ce mana ba zai yi tafiya ba, amma a yanzu yana tatata, kuma yana jan gindi, babban farin ciki na daya rayu, ina son abuna, kuma muna kaunarsa.” Inji mahaifiyar Tres

Zul waja haini: Yaro mai fuska 2 ya cika shekaru 13 (Hotuna)
Tres da Mahaifiyarsa

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan gida daya su 4, duk makafi

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng