Wasanni: ‘Yan kwallo 5 da su ka fi kowa albashi a Duniya

Wasanni: ‘Yan kwallo 5 da su ka fi kowa albashi a Duniya

– Babban Dan wasan Real Madrid Ronaldo ya fi kowa albashi a ‘Yan kwallo

– A bana kurum Ronaldo ya samu kudi har Dala Miliyan 88

– Lionel Messi ne ya zo na biyu a jerin

Mujallar Forbes ta fitar da wadanda su ka fi kowa albashi cikin ‘Yan wasa

Dan wasa Cristiano Ronaldo dai ya kerewa kowa a maganar kudi

Ronaldo na Real Madrid ne Dan wasan Duniya yanzu haka

Wasanni: ‘Yan kwallo 5 da su ka fi kowa albashi a Duniya
'Yan wasa Messi tare da Ronaldo da Suarez

A jerin ‘Yan wasan kwallon da su ka fi kowa albashi a Duniya Cristiano Ronaldo ne kan gaba inda a bana kurum ya tashi da sama da Dala Miliyan 88. Dan wasa Lionel Messi na Barcelona ya hada Dala Miliyan 81 a wannan shekara.

KU KARANTA: An ba Najeriya sama da Dala Miliyan 43

Wasanni: ‘Yan kwallo 5 da su ka fi kowa albashi a Duniya
Cristiano Ronaldo da Messi sun fi kowa albashi

Sauran ‘Yan wasa irin su Neymar Jr na Barcelona, da kuma Gareth Bale na Real Madrid da ma Zlatan Ibrahimovich na Manchester United su na cikin wadanda su ka fi kowa albashi a Duniya a wannan shekara.

Kungiyar Real Madrid ce ta lashe kofin Champions league na 2017 bayan ta doke Juventus da ci 4-1 a Birnin Cardiff. Ronaldo ya kara nuna cewa ya cika gwarzo inda ya jefa kwallaye biyu. Dan wasa Ronaldo ne dai ya kara gamawa da kwallayen da su ka fi na kowa a Gasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Alakar shararriyar 'yar wasan nan T-boss da wani Sanata

Asali: Legit.ng

Online view pixel