Gwamnan jihar Sakkwato ya bada naira miliyan 4 kudin jinyar Maryam Abubakar (Hotuna)

Gwamnan jihar Sakkwato ya bada naira miliyan 4 kudin jinyar Maryam Abubakar (Hotuna)

- Gwamnan jihar Sakkwato ya bada tallafi kudi naira miliyon 4 don jinyar Maryam Abubakar

- Abubakar ta kai tsawon shekara guda tana jinya a wani asibitin da ke kasar Indiya

- Gwamnan Tambuwal ya bukaci al’umman musulmi da su saka Maryam cikin addu'a Allah Ya bata lafiya

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal ya bada tallafin kudi naira miliyan 4 domin taimakawa Maryam Abubakar dan asalin jihar wanda take fama da ciwon kansar hanta, kuma yanzu tana wani asibiti a kasar India inda a ke mata jinya.

Legit.ng ta ruwaito cewa al’amarin ita wannan baiwar Allah dai ta yi kamari ne kana aka kirkiro da maudu’in #SUPPORTMARYAM, wato a tallafa wa Maryan wanda .

Tambuwal ya bayyana niyyarsa na biya wa Maryam kudin jinyar a Sakkwato a ranar Talata, 6 ga watan Yuni ta hanyar bakin mai magana da yawun gwamnan Malam Imam Imam.

Gwamnan jihar Sakkwato ya bada naira miliyan 4 kudin jinyar Maryam Abubakar (Hotuna)
Maryam Abubakar dan asalin jihar Sakkwato wanda take fama da ciwon kansar hanta

Imam Imam ya bayyana cewa gwamnan ya bukaci al’umman musulmi da su saka Maryam cikin addu'a Allah Ya bata lafiya.

Gwamnan jihar Sakkwato ya bada naira miliyan 4 kudin jinyar Maryam Abubakar (Hotuna)
Maryam Abubakar na shirin cin abinci da wani dan uwanta

Imam ya ce: “Maryam na daya daga cikin mu kuma gwamnatin jihar zata yi duk abin da zai yiwu domin tabbatar da cewa ta samu cikakken lafiya.”

Gwamnan jihar Sakkwato ya bada naira miliyan 4 kudin jinyar Maryam Abubakar (Hotuna)
Maryam Abubakar a gadon ta na asibiti

KU KARANTA: Biki bidiri: Sanata Saraki zai aurar da babbar Ýarsa

Mai jinyar ta kasance ma'aikatan nas a babban asibitin jihar kuma dan asalin kauyen Gilbadi a karamar hukumar Gada.

Tun shekara 2016 ne Maryam ke fama da ciwon kansar hanta inda ta kai tsawon shekara guda tana jinya a kasar Indiya kuma ana bukatar naira miliyan 4 domin a yi mata tiyata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan komawar shugaba Buhari Landan don duba lafiyarsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel