Manyan ramuka sama da 170 ne a akan titin Zariya zuwa Kano (Hoto)
- Titin Zariya zuwa Kano na cigaba da laƙume rayuka ba dare ba rana
- Babbar titin da ta hada garin Zariya zuwa Kano na cikin mawuyacin hali
Babbar titin da ta hada garin Zariya zuwa Kano na cikin mawuyacin hali, wanda sakamakon haka, tarin rayuka da dimbin dukiya ke salwanta sakamakon lalacewar hanyar a duka hannayen guda biyu.
Jaridar Premium Times tayi wani nazari akan hanyar, inda wakilinta ya bi titin Kaduna zuwa Kano, kuma ya kididdiga manyan ramukan kan titi masu zurfi wadanda ke haddasa munanan hadurra a kan titi.
KU KARANTA: Wani Fasto a Kaduna ya ciyar da Musulmai 500 a watan Ramadana
Ko akan hanyarsa ta shiga Kano a daidai kwanar Dangora bayan ya wuce Zaria, sai daya ya samu wata motar kamfanin Coca Cola ta yi hadari, kuma ana ta faman tattara kwalaben Coca Cola na roba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Majiyar Legit.ng ba tayi kasa gwiwa ba inda ta hada da kidayan motocin da suka yi hadari da ke can gefen titi a kwarankwatse.
Daga Kwanar Dangora zuwa Ciromawa, tafiyar ba ta wuce kilomita saba’in ba, amma an lissafa manyan ramuka masu kayar da mota komin girman ta, har guda 170, kuma a hannu guda kenan.
Da fatan gwamnati zata shigo cikin lamarin domin kawo agajin gaggawa ga wannan titi mai muhimmanci ko za’a rage samu yawan salwantar rayuka da dukiyoyi akan hanyar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Yaushe Buhari zai dawo?
Asali: Legit.ng