Gada ya fadi a jihar Niger (HOTUNA)
1 - tsawon mintuna
Wani gada ya fadi a kauyen Gidan Mai dake hanyar Mokwa-Makera sakamakon ruwan sama da aka sharara kamar da bakin kwarya. Wannan ya hana motoci tafiya daga bangarorin guda biyu.
Hukumar dake kare afkuwar hadurra ta Najeriya (FRSC), Mokwa, ta saki hotunan gadar da ya rufta a jihar a shafinta na Facebook.
Babu shakka faduwar gadar zai shafi kaiwa da komowa a ciki da wajen garin.
Ga hotunan gadar da ya fadi a kasa:
A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar FRSC sun bayyana cewa zasu bar hanyoyin jiha a Lagas kamar yadda gwamnan jihar, Akinwumi Ambode ya bukata.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng