Yan matan Chibok 2 sun karasa karatunsu a Amurka (Hotuna)

Yan matan Chibok 2 sun karasa karatunsu a Amurka (Hotuna)

Wasu yan matan Chibok 2 wadanda suka samu tserewa daga hannun Boko Haram sun karasa karatuna a makarantan American High School da ke kasar Amurka.

Yan matan masu suna Debbie da Grace sun karashe karatun sakandare ne a babban makarantan da ta shahara a Washington DC.

Wata jawabin da diraktan kungiyar bayar da agajin karatu EMC, Emmanuel Ogebe, ya saki, yace Debbie da Grace na cikin yan mata 57 da suka fara kubuta daga hannun yan Boko Haram bayan anyi garkuwa da su a watan Afrilun 2014.

Yan matan Chibok 2 sun karasa karatunsu a Amurka (Hotuna)
Yan matan Chibok 2 sun karasa karatunsu a Amurka (Hotuna)

Daga cikin wadanda suka halarci taron yan Najeriya sune shugabannin kungiyar EMC, Mr and Mrs Paul Gadzama da kuma wadanda suka zo daga Chibok.

KU KARANTA: Rikici tsakanin Yahaya Bello da Melaye tayi kamari

A jawabin yan matan, sun mika godiyansu ga wadanda suka dauki nauyinsu da kuma wadanda suka taimaka musu wajen cimma burinsu a rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel