Goron Ramadan: Ayyuka 3 da ya kamata mai azumi ya kiyaye
– Yayin da Musulmai ke ibadar azumi a fadin Duniya
– Akwai abubuwan da ya kamata mai azumi ya lura da su
– Ana dai sa ran gafarta zunubai a cikin wannan wata mai alfarma
Jiya kun ji cewa ya kamata a rika samun abinci mai lafiya a wannan wata
Haka kuma ya zama dole a kiyaye duk wani sabo a cikin watan
Ana bukatar a dage wajen ibada domin a samu rahama
1. Kiyaye sabo
Dole a guji duk wani aikin sabo na magana ko gani ko saurara. Hakan dai na iya nakasa azumin mutum idan ba a kula ba.
KU KARANTA: Abubuwan da ya dace a ci da azumi
2. Ayyukan lada
Haka kuma sai an dage da ayyuka na lada domin a samu ran tsira da dacewa cikin wadanda za a ‘yanta a cikin wannan wata.
3. Tsaida Sallah
Ta tabbata cewa duk wanda yayi azumi bai kiyaye ba zai kare da shan wahalar banza ba tare da wani lada ba. Dole mai azumi ya rike sallalin wajibi sannan kuma ya dage wajen sallolin nafila a Ramadan.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Za ka iya auren 'Yar wata kabila?
Asali: Legit.ng