Sa’ar bokan dake baiwa ýan-Fashi asirin sa’a ya ƙare

Sa’ar bokan dake baiwa ýan-Fashi asirin sa’a ya ƙare

- Wani boka daya kware wajen baiwa yan fashi sa’a ya shiga hannu

- N30,000 nake amsa a hannun ýan-Fashi don in yi musu addu’ar samun sa’a – Boka

Allah ya tona asirin wani boka daya kware wajen baiwa yan fashi sa’a mai suna Abdulrazak Buhari dake Sabon Gida jihar Katsina, inda shi kansa sa’arsa ta kare, ya shiga hannun jami’an Yansanda.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan boka shike yi ma yan fashin dake tare hanyar Funtua zuwa Zaria aiki, kuma boka Buhari ya bayyana ma jaridar cewar N30,000 yake amsa daga hannun barayin a duk aikin da yayi musu.

KU KARANTA: Sojojin Turkiyya 13 sun salwanta a hatsarin jirgin sama

“Maganan gaskiya, an kama ni ne sakamakon alakata da wasu yan fashi, kuma suna ajiyan buhunan shinkafar sata a gida na, sa’annan ina yi musu addu’ar samun sa’a. sau biyu kenan idan sun dawo daga fashi suna bani N30,000 da N20,000.” Kamar yadda ya shaida ma majiyar Legit.ng.

Sa’ar bokan dake baiwa ýan-Fashi asirin sa’a ya ƙare
Yansandan Najeriya

Dayake karin haske, kaakakin rundunar Yansandan jihar Katsina, DSP Gambo Isah yace rundunar tasu ta kama mutane 5 daga cikin gungun barayin, inda ta kwato buhunan shinkafa 48 daga gidan bokan.

Idan ba’a manta ba, ko a satin data gabata sai da Yansanda suka kama wani kasurgumin dan fashi mai suna Abdulaziz Ibrahim daga jihar Zamfara, daga nan kuma yayi sanadiyyar kamo sauran abokan nasa

Yan fashin sun yi ma wani mai suna Salisu Suleiman fashi akan hanyar Funtua inda suka kwace masa motar da ta kai Naira miliyan 2, haka zalika sun kwaci N100,000, motoci 2 da wayoyi 3 daga hannun mutane daban daban.

Da aka tsananta bincike, an gano bindiga, harsashai da alburusai, adduna da sanduna, fitila da sauran kayan tsafe tsafe duk a gidan barayin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An bayyana nasarorin Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng