Buhari ne zai kai Najeriya ga ci, inji Sarkin Auchi ta jihar Edo
- Ana yabawa da mulkin Buhari a cikarsa shekaru biyu a kan mulki
- Buhari na shan suka daga wasu bangarori na kasar nan
- Sarkin Auchi ya yaba wa shugaba Buhari
A cikarsu shekaru biyu a kan mulki, shugaba Buhari ya sami yabo daga sarkin Auchin jihar Edo, mai martaba Sarki Alh. Aliru Momoh Ikelebe na III, inda yace kuncin da aka sha a wannan mulkin gini ne na abubuwan alheeri wadanda za'a girba nan gaba.
Otarun Auchin yace Buhari nayi wa kasar nan tanadi mai-kyau ne, kuma ya kawo canji a kasa. Ya fadi hakan ne a lokacin ziyarar gwaman jihar na APC da keyi ta shan ruwan azumi a fadarsa.
Ziyarar ta hada da mataimakin gwamnan jihar Malam Philip Shuaibu, a yayin shan ruwa da sarakunan gargajiya na yankin.
'Shugaba Buhari ya kawo ci gaba da chanji kasar nan, kuma ma duk inda yaje a kasashen waje, sai san barka da yake sha da tarba mai kyau'.
Ya kuma yi wa shugaban fatan nasara da karin lafiya.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng