Gwamnatin jihar Sokoto zata kashe N566miliyan wajen gyaran masallatai 189

Gwamnatin jihar Sokoto zata kashe N566miliyan wajen gyaran masallatai 189

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya amince da fitar da zunzurutun kudi har N566 miliyan domin gyaran masallatai 189 na juma'a a dukkan fadin jihar wadan da ya gada daga tsohuwar gwamnati.

Kwamishinan harkokin addini na jihar Alhaji Mani Maishinku Katami shine ya bayyana hakan ga manema labarai a lokacin da yake kaddamar da shirin Kwamitin Zakka da wakafi na rarraba kayayyaki ga mabukata a garin Illela.

Legit.ng ta samu labarin cewa Kwamishinan ya kara da cewa tundaga 2015 zuwa yanzu gwamnati ta kashe kudin da suka kai N805 miliyan wajen harkokin addini.

Gwamnatin jihar Sokoto zata kashe N566miliyan wajen gyaran masallatai 189
Gwamnatin jihar Sokoto zata kashe N566miliyan wajen gyaran masallatai 189

A nashi jawabin, shugaban ma'aikatar ta zakka da wakafi Malam Lawal Maidoki ya bayyana cewa marayu 18,200 ne hukumar ta samar wa da kayan sawa da kuma abinci isasshe a lokacin azumin nan da kuma shagulgulan sallah.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: