An kamo yar Fim ɗin Hausa a aka yanke ma hukuncin kisa, amma ta arce daga gidan yari (Hoto)

An kamo yar Fim ɗin Hausa a aka yanke ma hukuncin kisa, amma ta arce daga gidan yari (Hoto)

- Rabi Isma'il yar fim din Hausa data kashe saurayinta ta kuma shiga hannu

- Rabi ta kashe saurayin nata ne a shekarar 2005

Wata tsohuwar yar Fim din Hausa Rabi Isma’il data taba tserewa daga gidan yarin garin Hadejia na jihar Jigawa a ranar 16 ga watan Daisambar 2011 ta shiga hannu, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Ita dai Rabi Isma’il an yanke mata hukuncin kisa ne a ranar 5 ga watan Janairun shekara 2005, amma sai aka jefar da ita a gidan yarin Hadejia, inda daga nan ne ta tsere, sai dai a jiya ne jami’an tsaron sirri tare da hadin gwiwar ma’aikatan gidan yarin suka sake shako wuyanta.

KU KARANTA: Sabo da kaza: Damisa ta kashe mai kula da namun daji

Yayin rikicin shari’ar nata har sai da aka kai ga kotun koli, wanda ita ma ya tabbatar mata da hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kashe saurayinta da tayi mai suna Auwalu Ibrahim ta hanyar bashi kwayoyi, sa’annan ta nutsar da shi duk wai don ta gaji kadararsa.

An kamo yar Fim ɗin Hausa a aka yanke ma hukuncin kisa, amma ta arce daga gidan yari (Hoto)
Rabi Isma'il

Shugaban hukumar kula da gidajen yari ta kasa ya yaba da hadin gwiwar da jami’an tsaron sirri dana Yansanda suka basu don kamo Rabi, daga nan sai ya roki jama’a da su dinga jiyar da jami’an tsaro bayanai kan duk wasu miyagun mutane da suka sani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli abinda wani yace game da shuwagabannin mu

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng