'Yar talakawa ta ci kyautar Naira miliyan 6 a gasar Kimiyya

'Yar talakawa ta ci kyautar Naira miliyan 6 a gasar Kimiyya

- Morufat Lawal taci gasar kudi har naira miliyan shida

- Ta nuna bajintarta a bangaren lissafi

- Yarinyar ta buge mutane 40 ta lashe gasar

A gasar da aka yi a jihar Oyo, a kudancin Najeriya, wata 'yar karamar yarinya ta lashe gasar zunzurutun kudi har naira miliyan shida a gasar kimiyya ta lissafi, inda ta doke mutum 40 kafin ta cinye gasar, a wata bajinta da aka dade ba'a gani ba a jihar.

Yarinyar dai 'yar talakawa ce kuma 'yar kauye, amma ta nuna kwazo da hazaka a gasar, 'yar asalin Fidiki, maraya a cikin jihar Oyo.

KU KARANTA KUMA: Jihar Sakkawato ta ɗauki nauyin mata 200 domin koyan likitanci

'Yar talakawa ta ci kyautar Naira miliyan 6 a gasar Kimiyya
'Yar talakawa ta ci kyautar Naira miliyan 6 a gasar Kimiyya

Ta lashe kyautar ta gasar kasa baki daya, bayan da ta buge yaran masu kudi daga makarantun masu kudi, kuma taci kyautar kudin har Naira miliyan shida.

Ana yawan samun irin wadannan yara dai a Najeriya, sai dai ba safai suke samun tallafi don su zama wasu masu tabukawa kasa komai ba, sai dai alkawurra na siyasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Legit.ng ta kawo maku bidiyon da hukumar DSS ta mika 'yan matan Chibok 82 da aka ceto ga gwamnatin tarayya:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng