Allura-ta-tono-galma: Kotu tayi ram da wani da ya ba yan sanda kwarmaton karya

Allura-ta-tono-galma: Kotu tayi ram da wani da ya ba yan sanda kwarmaton karya

Wata kotun Majistare dake a garin Abuja ta gurfanar da wani matashi mai suna Ahmed Echoda yayin da kuma daga baya ta makashi a kurkuku saboda bayar da kwarmaton karya ga jami'an yansanda wadanda suka je bincike gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu.

Shi dai Ahmad Echoda an gurfanar da shi din ne a jiya inda kuma aka tuhume shi da bayar da bayanan karya ga jami'an yan sandan Najeriya tare kuma da yaudarar su.

Legit.ng ta samu labarin cewa duk da dai cewa su biyu ne ake zargin amma dai shi Ahmad din shi ne kadai ya gurfana a gaban kotun.

Allura-ta-tono-galma: Kotu tayi ram da wani da ya yan sanda bada kwarmaton karya
Allura-ta-tono-galma: Kotu tayi ram da wani da ya yan sanda bada kwarmaton karya

Da ake karanta masu laifukan nasu, Echodo da kuma Maiwada Adamu ance sun hada kai ne inda kuma suka yaudari yan sanda da bayanin da suka bada na cewa wai akwai muggan makamai a gidan Ike Ekweremadu.

A nashi bangaren Echodo ya musanta laifin dake tuhumar sa da shi wanda dalilin hakan ne sai kotun ta tura shi a gidan yari har zuwa 6 ga watan Yuni domin ci gaba da shari'ar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng