'A girmama dokar kotu a saki El-zazzaki, da Dasuki' - Itse Sagay

'A girmama dokar kotu a saki El-zazzaki, da Dasuki' - Itse Sagay

- An garkame Zakzaki tun karshen 2015, bisa zargin ta'addanci

- An kame Dasuki tun hawan Buhari, bisa zargin wawason kudin gwamnati

- An sha bada odar a sako su amma gwamnati tayi biris da batunsu.

Farfesa Itse Sagay, mai shugabantar kwamitin shugaban kasa kan yaki da tu'annati da kudin kasa, kuma babban lauya, SAN, yace ya kamata gwamnati ta girmama kotu ta sako su Dasuki da Zazzaki, tunda kotu tace a sako su, ya ce 'ina mamakin dalilin rufe su din, duk da cewa an ce a sako su.

Makudan kudaden kasa ne dai ake zargin tsohon soja kuma tsohon mai tsaron kasa da wawure wa da raba wa jama'a, kuma duk da cewa tsohon shugaba Jonathan ne ya rattaba hannu a duk takardun, shi kadai yake shan bugu a hannun hukuma.

KU KARANTA KUMA: Ka yi mun gani, sai dai...: ‘Yan adawa sun yabawa Shugaban kasa Buhari

Shi kuma Malam Zazzaki, shugaban kungiyar IMN mai son kawo shari'ar musulunci ga Najeriya, ana tuhumarsa ne da kokarin tada zaune tsaye, da kuma ta'addanci, abin da lauyansa ya musanta. Ana dai zargin sojoji da kashe dubban mabiyansa a shekarar 2015 da 2016, kuma ko a baya ma, tsohon shugaban mulkin soja Gen. Sani Abacha ya kulle shi, shekaru da dama, bisa irin wannan zargi.

Itse Sagay dai, dama wasu da dama sun sha kiran a sako wadannan kamammu, amma gwamnati tace sakinsu yana da hadari sosai, don haka ta ci gaba da kulle su.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo da Legit.ng ta kawo ma ku:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng