Barayin da suka saci shanu 334 a Neja sun shiga hannu

Barayin da suka saci shanu 334 a Neja sun shiga hannu

- Rundunar Yansandan jihar Neja ta kama wasu gaggan barayin shanu

- Hukumar yansandan ta kama wasu gaggan yan fashi guda hudu

Rundunar Yansandan jihar Neja ta kama wasu gaggan barayin shanu su uku da suka sace shanu 334 a garin Bangoli na karamar hukumar Kwantagora jihar Neja. Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kaakakin rundunar aynsandan jihar Neja, DSP Bala Elkana yace barayin shanun yan wata gungun barayi ne mai mutane 40 da suka addabi yan kauyen, inda suke fakewa dajin Kabaro na jihar Zamfara.

KU KARANTA: Yan Najeriya sun gamsu da kamun ludayin gwamnatin mu – Osinbajo

Barayin shanun sun hada da Haruna Muhammed, Tukur Hassan da Adamu Gurmu, inji rahoton majiyar Legit.ng.

Bugu da kari, hukumar tace ta kama yan wasu gaggan yan fashi guda hudu a garin Minna da wasu masu garkuwa da mutane a garin Lambata, dake karamar hukumar Gurara.

Barayin da suka saci shanu 334 a Neja sun shiga hannu
Yansanda a bakin aiki

DSP Elkana yace yan fashin da aka kama dalibai ne a jami’a kimiyya da fasaha dake Minna, inda yace sun yi ma wani mutum mai suna Nwosu Stephen fashi, inda suka kwace masa na’urar tafi da gidanka da darajar tat a kai N130,000 da wayoyi gida 2.

“Yayin da muka samu labarin yan fashin, sai jami’an mu suka dira mafakar su, inda aka yi dauki ba dadi tsakanin bangarorin biyu, sakamakon haka an raunata yan fashi biyu, biyu kuma sun tsere. Sa’annan mun kwato bindiga kirar AK 47 guda 2.” inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kasa daya al'umma daya, Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel