Paul Pogba: Ɗan ƙwallon da yafi riƙo da addinin Musulunci
- Shin Pogba Musulmi ne? da gaske yaje Umrah? Shin yana Azumi? Ko kuwa yana Sallah?
- Paul Pogba Musulmi ne, kuma yana Sallah da Azumi
A yan kwanakin nan an samu rahotanni da dama dake nuna fitaccen dan kwallon kungiyar Manchester United kuma dan kasar Faransa, Paul Pogba yayin dayake Umrah, hakan ya taso da batutuwa da tambayoyi da dama, kamar su:
Shin Pogba Musulmi ne? da gaske yaje Umrah? Shin yana Azumi? Ko kuwa yana Sallah? Toh ga amsoshin ku nan kamar yadda Legit.ng ta samo.
KU KARANTA: Sabuwar doka: An haramta sakin aure a watan Ramadan a wata ƙasar Larabawa
Paul pogba wanda ya ja zarensa a harkar kwallon kafa a duniya gaba daya dan kasra Faransa ne kuma dan asalin kasar Guinea ne, wanda a yanzu yake sana’ar taka leda a Manchester bayan ya rabu da Juventus.
Da gaske ne Paul Pogba na daya daga cikin shahararrun musulman yan kwallin duniya, kuma yana matukarkare addininsa da danginsa da al’ummarsa, Pogba mutum ne mai tsannain kaunar matarsa da yayansa.
Pogba ya gamsu da taimakon Allah, kuam ya yarda ba tare da taimakon Allah ba, ba inda za shi, sa’anan Pogba baya wasa da Sallah ko kadan, baya yarda a fara wasan kwallo face ya gabatar da sallar sa, sa’annan kuma shi mai yawan yin addu’a ne kafin kowane wasa.
Haka zalika kan maganan Azumin watan Ramadana, an san Azumi na hana cin abinci, don haka mutum zai iya samun kasala, amma kuma bincike ya nuna yan wasa musulmai da dama basa shan Azumi don yunwa, sai dai hakan ya danganta ga mutum ne kawai, don haka Pogba baya wasa da Azumi, don har Umrah yaje.
Pogba yace “Ban taba jin dadi a rayuwa ba irin na gannin ina gudanar da aikin Hajji ko Umrah” da wannan zamu tabbatar da cewa, eh, Pogba Musulmi ne, kuma mai kare dokokin Musulunci bakin gwargwado.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng