Ayyuka 10 da gwamnatin Sakwato ta kaddamar a ranar demokradiyya (Hotuna)
- Gwamnan jihar Sakkwato ya kaddamar da wasu ayyukan gwamnati 10 don inganta rayuwan al’umman jihar
- An kaddamar ayyukan ne don murnar bikin ranar demokradiyya da kuma cika shekara biyu a mulki
- Gwamnan kuma ya rarraba wasu gidajen wuta 172 na iya aiki daban-daban wa al'ummomin jihar a wasu makonin da ta gabata
A ranar Litini, 29 ga watan Mayu kuma ranar demokradiyya a kasar Najeriya ne gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da wasu muhimman ayyukan gwamnati 10 a fadin jihar a wani bangaren murnar bikin ranar demokradiyya da kuma murnar cika shekara biyu a matsayin gwamnan jihar.
Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Sakkwato a wasu makonin da ta gabata ta rarraba wasu gidajen wuta 172 na iya aiki daban-daban wa al'ummomin jihar don bunkasa wutar lantarki a yankin.
Gwamnatin kuma ta bada kyautar filin gina gidajen shirin gwamnatin tarayya a jihar da nufin marawa gwamnatin tarayya baya don iganta rayuwan al’umman jihar.
Ayyukan da gwamnan ya kaddamar sun hada da:
1. Sanata Adamu Aliero ya kaddamar da bude kamfanin samar da taki wato Sokoto-IML Organic fertiliser factory
2. Gwamna Tambuwal ya gabatar da motocin bas 45 da kuma kayan karatu ga makarantun sakandare
3. Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar kuma ya bude tagwayen titin nan da aka sani da Sultan Ibrahim Dasuki
4. Shi kuma tsohon gwamnan jihar Sakkwato a karkashin mulkin soja Navy Kyaftin Raji ya bude sabon dakin karatu da kuma wasu hadaddun azuzuwa a kwalejin kiwon lafiya da ke Swakkato.
5. Tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai, Honorabul Emeka Ihedioha ya bude babban titin kewaya ta yamma da kuma hanyan bankin Keystone.
6. Honorabul Emeka Ihedioha ya kuma bude Gidan Dare roundabout da hanyan kamfanin Sakkwato Furniture.
KU KARANTA: Wani dan majalisa ya raba kaya na kimanin milyan 150 ga al'ummar mazabarsa (Hotuna)
7. Tsohon gwamnan jihar arewa maso yamma, CP Usman Farouk mai Ritaya ya bude
Government Secondary School Gumbi wanda aka gyra.
8. CP Usman Farouk kuma ya kaddamar da na’urar haska bayanai tarin na dalibai
9. Bude goverment Model School, Tudun Wada, Sakkwato
10. Bude hanyan sabon birni
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga bidiyon inda mai martaba sarki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari
Asali: Legit.ng