Hadarin mota ya rutsa da 'Yan Mata masu tallace-tallace a Kano

Hadarin mota ya rutsa da 'Yan Mata masu tallace-tallace a Kano

- Wani mummunan hadari ya afku a kusa da Sabon titin Fanshekara kan hanyar zuwa Madabi, dake jihar Kano

- Hadarin ya ritsa da wasu 'Yan Matan masu tallace-tallace kan hanyar su ta komawa gidajan su

- 'Yan Matan masu talla kusan 15 ne suka rasa ransu yayinda wasu kuma suka jikkata

Wani mummunan hadari ya afku a kusa da Sabon titin Fanshekara kan hanyar zuwa Madabi, dake jihar Kano.

Hadarin ya ritsa da wasu 'Yan Matan masu tallace-tallace kan hanyar su ta komawa gidajan su, wanda mafi yawan cin su sun fito ne daga kauyukan dake yamman da cikin kwaryar birnin Kano, kamar Calawa, Maraya, Madobi, Yako, Watari, da sauran su.

Masu talan kan fito tun sanyin safiya sannan su shiga unguwanni, kasuwanni, asibitoci da sauran gurare domin tallata hajar da suka kawo irin su gyada, zogale, rama, mangwaro, albasa da sauran su.

KU KARANTA KUMA: An hurowa Gwamnan Legas wuta (Abin da ya faru zai ba ka mamaki)

Hadarin mota ya rutsa da 'Yan Mata masu tallace-tallace a Kano
Hadarin mota ya rutsa da 'Yan Mata masu tallace-tallace a Kano

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya yi kira ga sadaukarwa, da kuma yi ma Buhari addu’a a cikin sakon ranar demokradiyya

Legit.ng ta samu labarin cewa take a nan take aka samu asarar rayukan 'Yan Matan kusan 15 yayinda wasu kuma da dama suka jikkata sakamakon motar su da suke ciki ta yi gaba da gaba da wata babbar mota kamar yadda wanda abin ya faru a ga bansa ya shaida.

Allah ya gafartawa wadanda suka riga mu gidan gaskiya, masu jikkata kuma Allah ya basu lafiya

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan kasuwa sun koka kan yadda abubuwa ke tafiya a Najeriya"

Asali: Legit.ng

Online view pixel