Ana murkushe Inyamurai a Najeriya – Inji tsohon Gwamnan Imo

Ana murkushe Inyamurai a Najeriya – Inji tsohon Gwamnan Imo

– Inyamurai sun kara kokawa cewa lallai ana danne su

– Wani tsohon Gwamnan Jihar Imo yace Gwamnatin Tarayya ba ta masu adalci

–Tsohon Gwamnan Jihar Imo Ikedi Ohakim ya fadi wannan

Inyamurai dai su na kuka da wannan tsari na Gwamnatin Tarayya.

Da dama suna cewa ana murkushe su har wasu na nema a raba kasar.

Wani tsohon Gwamnan Anambra yayi kaca-kaca da Shugaba Buhari kwanaki

Ana murkushe Inyamurai a Najeriya
Ana danne Inyamurai a kasar nan – Inji wani tsohon Gwamna

Tsohon Gwamnan Jihar Imo Ikedi Ohakim yace dole ayi sauyi a harkar siyasar kasar nan domin kuwa ana murkushe 'Yan kabilar Ibo. Ohakim yayi wannan kira ne a wani taro da aka yi a dakin taro na Chinue Achebe a Garin Nsukka.

KU KARANTA: Masana na da shakka game da tarihin Bayajidda

Ana murkushe Inyamurai a Najeriya – Inji tsohon Gwamnan Imo
An danne Inyamurai a kasar nan – Inji tsohon Gwamna Ohakim

A cewar tsohon Gwamnan, matsin tattalin arzikin da aka shiga ya kuma fi shafan Inyamurai. Ohakim yace Yankin Kasar Ibo na bin Gwamnatin Tarayya wasu bashin kudi tun lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo wanda za su nemi a fito masu da hakkin su.

Kwanaki Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Balarabe Musa yace dole Inyamurai su nemi a raba Najeriya don suna jin cewa an maida su saniyar ware a Najeriya. Tsohon Gwamnan yace bai yi mamaki da ya ga wasu sun hakikance sai an samar da Kasar Biyafara ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Obasanjo yayi magana wajen bikin Biyafara

Asali: Legit.ng

Online view pixel