Kocin Arsenal Arsene Wenger ya kafa tarihi a Ingila
– Kungiyar Arsenal ta ba Chelsea kashi jiya
– Arsenal ta dauki kofin FA a filin Wembley na Ingila
– Dan wasa Aaron Ramsey ya ceci Arsenal
Duk Ingila babu Kocin da ya dauki Kofin FA irin Wenger
Arsenal na da Kofin FA 13 a Tarihi
Kungiyar Arsenal ta sha gaban Manchester United
Arsene Wenger ya zama Kocin da ya fi kowa lashe kofin FA na Ingila jiya bayan ya dauko kofin sa na 7. Wenger ya dauki kofin sau 3 kenan cikin shekaru 4 da su ka wuce wanda ya sa Arsenal ta fi kowa yawan kofin na FA har 13.
KU KARANTA: Kyawawan hotunan Kiki Diyar Osinbajo
Dan wasan Najeriya da ke Chelsea Victor Moses dai ya ji kunya a wasan inda ya sha jan kanti bayan yayi kokarin yin wani lambo. Dan wasan tsakiya Aaron Ramsey na ya ci wa Arsenal kwallon karshe wanda ya tabbatar cewa Kungiyar ita ma taci kofi bana.
A makon jiya Real Madrid ta lashe gashe gasar La-liga karo na farko cikin shekaru wajen 5. Koci Zinedina Zidane ya dauki kofin sa na 4 a kulob din bayan Real Madrid ta doke Malaga a wasan karshe.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ko duka na sa mutum ya bar gidan aure?
Asali: Legit.ng