An bude babban masallacin juma'an da gwamnan Bauchi ya gina (Hotuna)

An bude babban masallacin juma'an da gwamnan Bauchi ya gina (Hotuna)

- Gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ya gina wani babban masallaci a Bauchi wanda aka bude a ranar juma’a da ta gabata

- Babban masallacin na daya daga cikin manya-manyan masallatai masu tarihi a Jihar Bauchi

- Mazaunan unguwan da aka gina masallacin sunyi fatan alkhairi ma gwamnan kan gina wannan masallaci

An budi babban Masallacin juma'an da gwamnan Bauchi ya gina a kofan Galadiman Bauchi a ranar juma’a 26 ga watan Mayu.

Mai girma gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ya bude babban masallacin juma'a daya gina a kofar gidan Galadiman Bauchi, a unguwan jahun da ke cikin garin Bauchi.

Wannan babban masallacin Galadima tana daya daga cikin manya manyan masallatai masu tarihi a Jihar Bauchi.

An bude babban masallacin juma'an da gwamnan Bauchi ya gina (Hotuna)
Gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ke magana a lokacin bude masallacin juma'a da ya gina a Bauchi

KU KARANTA: Hajjin bana: Mahajjata za su biya naira 38,000 kudin hadaya

Dubban jama'a ne suka halarci wannan budi masallaci cikin su manya manyan mutanen da suka halarci wannan budi masallaci har da mai martaba sarikin Bauchi injiniya Alh. Dakta Rilwanu Suleiman Adamu da kuma Galadiman Bauchi Alh. Ibrahim Saidu Jahun.

An bude babban masallacin juma'an da gwamnan Bauchi ya gina (Hotuna)
Galadiman Bauchi Alh. Ibrahim Saidu Jahun ke magana a bikin bude masallacin

Jama'an wannan unguwa sunyi ta fatan alkhairi ma gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar a kan wannan aiki na gina wannan masallaci.

An bude babban masallacin juma'an da gwamnan Bauchi ya gina (Hotuna)
Al'umman musulmai a wajen bude masallacin

An bude babban masallacin juma'an da gwamnan Bauchi ya gina (Hotuna)
Mai martaba sarikin Bauchi injiniya Alh. Dakta Rilwanu Suleiman Adamu (tsakiya), gwamnan Bauchi da kuma Galadiman Bauchi

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon tsohon direban Bishof David Abioye wanda ya karbi musulunci yayin da ya yi murabus da cocin Living Faith Church

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: