Gwamnatin jihar Sokoto ta bankado ma’aikatan bogi 13,415

Gwamnatin jihar Sokoto ta bankado ma’aikatan bogi 13,415

Gwamnatin jihar Sokoto tace ta cire sunayen mutane 13,415 daga cikin jerin wadanda ake biya albashi a kananan hukumomi 23 a fadin jihar.

NAN ta bada rahoton cewa kwamishanan kananan hukumomi , Alhaji Mannir Dan-Iya, ya bayyana wannan ne yau Alhamis a jihar.

Kwamishanan wanda yayi bayani ga manema labarai kan ayyukan ma’aikatar yace cikin shekaru 2 da suka gabata, an gano sunayen ne yayinda ake kuntata ma’aikata a 2016 da 2017.

Yace: “Bayan gudana 2, an bankade kananan ma’aikata 12, 915 wanda ya kunshi maras zuwa aiki da kuma na bogi.

Gwamnatin jihar Sokoto ta bankado ma’aikatan bogi 13,415
Gwamnatin jihar Sokoto ta bankado ma’aikatan bogi 13,415

” Hakazalika, an gudanar da na manyan ma’aikata inda aka cire sunaye 500 wanda ya kunshi ma’aikatan da suka isa murabus, matattu, da na bogi daga cikin lissafi.”

Dan-iya ya kara da cewa gwamnati ta zamar da biyan albashi hakane saboda bayyana gaskiya. Yace a yanzu ana biyan kudi cikin asusun ajiyan bankin mutane ne kai tsaye.

KU KARANTA: An kafa kwamitin kara albashin ma'aikata

Kwamishanan ya tabbatarwa wadanda akayi kuskure wajen cire sunayensu cewa za’a gyara shi.

Kwamishanan yace an raba magunguna na kimanin kudi N165million ga kananan hukumomi 23 domin tabbatar da kiwon lafiya.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel