Anyi ma wani malami ɗan Najeriya kyautan N12,000,000 a kasar Birtaniya

Anyi ma wani malami ɗan Najeriya kyautan N12,000,000 a kasar Birtaniya

- Wani dan Najeriya dake koyarwa a kasar Ingila yayi bajinta

- An karrama wannan malami da kyautar naira miliyan 12

Wani malamin lissafi ɗan Najeriya, Godwin Benson, ya samu kyautar Dala dubu 32 (kimanin Naira miliyan 12) daga Kungiyar Injiniyoyi ta Birtaniya wato UK Royal Academy of Engineering, inji rahoton BBC Hausa.

Malami Godwin ya cancanci kyautar ne sakamakon kirkiro wani shafin intanet da yayi mai suna ‘Tuteria’, wanda yake taimakawa iyaye wajen samarwa 'ya'yansu malamai da za su rika koyar da su darussa a gida.

KU KARANTA: Mabiya addinin Shi’a sun gindaya ma gwamnati matakan yin sulhu

Da aka tambaye shi, Malam Godwin yace ya fara tunanin kafa shafin ne yayin da yake koyar da darasin lissafi:

Anyi ma wani malami ɗan Najeriya kyautan N12,000,000 a kasar Birtaniya
Godwin Benson

"A lokacin mun yi yarjejeniya da mahaifin wani dalibina kan zai rika biyana dubu shida a ko wanne wata idan na koyar da ɗansa, amma sai mutumin ya yaudare ni, yaki biyana," in ji Godwin.

Daga nan ne sai Malam Godwin ya fahimci cewa mutumin ya kwashe wata da watanni yana neman malamin da zai rika koyar da dansa a gida, ba tare sanin cewa Mista Godwin yana kusa da unguwar da yake ba.

Duk da cewa sun samu matsala da mutumin, daga nan ne a shekarar 2015 Godwin ya fara tunanin buɗe shafin Intanet da zai rika sadar da iyayen yara da malamai masu koyar da yara darussa a gida.

Malam Godwin yace duk iyayen dake bukatar malamai za su iya bayyana hakan ne tashafin na Tuteria kuma su biya kudin kama aiki da za’a baiwa malaman don samun kwarin gwiwar fara aiki.

Majiyar Legit.ng ta bayyana shugaban kungiyar Injiniyoyin Malcolm Brinded, yace shafin Intanet din Godwin ya sauya yadda 'yan Najeriya suke samun ilimi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hanya mai sauki na rage kiba

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng