Dalilan kin sakin Dasuki da El-Zakzaki – Inji gwamnatin tarayya

Dalilan kin sakin Dasuki da El-Zakzaki – Inji gwamnatin tarayya

- Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da yasa suka ci gaba da tsare Kanal Sambo Dasuki mai ritaya da Ibrahim El- Zakzaky a gidan yari

- Gwamnati ta ce tana ba El- Zakzaky kariya daga barazanar da ke iya tashi sakamakon samun 'yanci, shi kuma Dasuki na da jerin shari’un da gwamnati

- Malam Garba Shehu ya ce za a amince da 'yancin Dasuki idan har an kai ga kammala daukacin shari’un da ke gabansa

A karon farko tun bayan garkamesu a gidan yari ba tare da beli ba, gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan ci gaba da tsare tsohon mashawarcin tsaro Kanal Sambo Dasuki mai ritaya da shugaban 'yan Shi'a Ibrahim El-Zakzaky.

Gwamnatin tarayya ta ce bata da niyayr musgunawa El-Zakzaky da ake cigaba da tsarewa a birnin Abuja. Sai dai kuma tana bashi kariya daga barazanar da ke iya tashi sakamakon samun 'yancinsa, a yayin da shi kuma Kanal Sambo Dasuki ke da jerin shari’un da gwamnatin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Jihohin Neja-Delta sun fi kowa samun kaso mai tsoka a Najeriya

Mataimakin na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya ce za a amince da 'yancin Dasuki ne kawai in har an kai ga kammala daukacin shari’un da ke gabansa a halin yanzu.

Jerin kotunan Najeriya dama na wajen kasar da suka hada da ita kanta kotun yankin yammacin Africa sun nemi sakin na Kanal Dasuki da ake zargi da almubazzaranci da kudin yaki da ta’addanci kusan dala Amueka biliyon 2.5.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yayin da aka gurfanar da jami'in INEC a kotu da ke Abuja

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng