Za a saukar da Alkur’ani mai tsarki 100 domin Buhari
- Gwamnatin jihar Zamfara ta shirya malamai masu karatun Alkur'ani 500 don saukar da Alkur’ani da kuma yin addua ga shugaba Buhari
- Masu karatun sun sauke Alkur'ani mai tsarki 100 daga daren Lahadi zuwa safiyar ranar Litinin
- Gwamnatin ta ce wannan na cikin shirin ayyukan murnan bikin ranar dimokuradiyya na 2017 a jihar
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce a ranar Talata, 23 ga watan Mayu cewa ta tattara malamai masu karatun Alkur'ani mai girma 500 don saukar da Alkur’ani da kuma yin addua musamman ga shugaban kasar Muhammadu Buhari da kuma kasar baki daya.
Legit.ng ta ruwaito cewa, kwamishinan karkara da kuma ci gaban al’umma, Alhaji Lawal Liman ya tabbatar da haka a Gusau birnin jihar Zamfara da cewa an gayyato malamai ne daga kananan hukumomi na jihar 14.
Kamar yadda kwamishinan ya bayyan, malaman Alkur’ani da aka kawo ya kazance a cikin shirin a matsayin wani bangare na ayyukan murnan bikin ranar dimokuradiyya na 2017 a jihar.
KU KARANTA KUMA: Shin ina shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake a yanzu?
Kwamishinan ya ce: "Idan shugaban kasar, a matsayinsa na shugaban Najeriya bai da lafiya, toh, ya kamata lamarin ya zama damuwar ga duk 'yan Najeriya domin lafiyarsa yana matukar muhimmanci a gare mu a matsayin mu na mutane da kuma a matsayin al'ummar kasar.”
Kwamishinan ya kara da cewa masu karatun Alkur'ani mai girma 500 wanda aka shirya a babban masallacin Gusau, sun sauke Alkur'ani mai tsarki 100 daga daren Lahadi zuwa safiyar ranar Litinin, 22 ga watn Mayu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Femi Fani Kayode ya bayyana cikakken bayani da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari
Asali: Legit.ng