Toh fa: Wani malami ya tilasta wata yarinya mai shekaru 14 auren dole (Hotuna)
- Wani bidiyon da ke yawo ta tona asirin baban malamin addinin musulunci yadda ya ke aurar da yara kanana ga mutane
- Malamin ya aurar da wata matashiya mai shekaru 14 ga wani mutumin da ya bata tazarar shekaru 20
- Iyalan ita yarinya sun amince da daurin auren yayin da ango mai jiran gado ya biyan iyalan da zinariya abun wuya
A cikin wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta inda aka tilasta wa wata yarinya mai shekaru 14 da haihuwa auren wani mutum musulmi wanda yaba yarinyan tazarar shekaru 20, an yi wannan daure auren dole ne a bayan gini masallaci Melbourne. Ango mai jiran gado ya ba iyalan yarinya zinariya abun wuya a madadin sadaki.
‘Yan sanda ne dai suka gano wannan bidiyo a cikin wayar tarho na mutumin wato angon ita yarinya wanda ya nuna bikin auren da aka yi ta hanyar addinin musulunci da wani shahararren malamin daure auren addini ya hada a bara.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, babaan malamin addini Imam Ibrahim Omerdic mai shekaru 62 a yanzu aka yana fuskanci zargi daga kotu a kan tilasta wa ‘yan mata kanana yin auren dole.
A cikin bidiyon da aka nuna a kotu wanda jaridar 7 News ta samu inda wata matashiya mai shekaru 14 ke zaune shurun yayin da angon ta ke rattaba hanun a wani takadar da imam din ya bashi.
KU KARANTA KUMA: Matashin yaro daga Adamawa ya ci 308 a jarrabawar JAMB ta 2017 (DUBA)
A cikin bidiyon uwar ita yarinya ma tana zaune tana kallo yada angon ‘yarta ya biya don ya aure ‘yar na su da zinariya abun wuya wanda ke dai dai da kudin dalla Amurka 1,480.
Imam din ya tambayi ita yarinya wato amarya cewa ko ta amince da mutumin a matsayin mai gidan ta kuma zata yi biyayya gareshi bisa koyarwar addinin musulunci inda ita kuma ta amince da haka.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ku kali wata yarinya makaniken mota a birnin tarayya Abuja
Asali: Legit.ng