Shin ina shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake a yanzu?

Shin ina shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake a yanzu?

- Anyi rade-radin shugaba Buhari ya mutu a baya, amma gwamnati ta fito ta musanta

- Anyi rade-radi cewa wasu na son su hada kai da soji don yin juyin mulki, amma wai an shawo kan lamarin inji shuwagabannin sojin Najeriya

- 'Yan Najeriya na tambaya wai ina shugaba Buhari ke jinya a Ingilar?

A shafukan sada zumunta, 'yan Najeriya na tambaya shin ina shugaban Najeriya Janar Buhari yake a yanzu?

Amsa da mataimakin shugaban kan harkokin sabuwar sadarwa, Ahmad Sadik ke amsawa da cewa, shugaban yana asibiti a ingila yana jinya, kafin kuma ya tafi, ya rubuta wasika zuwa ga majalisa, 7 ga watan Mayu, sannan ya furta cewa shugaban bai san rananr dawowarshi ba, sai fa idan ya warke, likitoci sun sallamo shi.

Shin ina shugaban Najeriya Janar Buhari yake a yanzu?
Shin ina shugaban Najeriya Janar Buhari yake a yanzu?

A dai sati biyu da shugaban bayanan, anji rade-radin wai ya rasu a asibiti, inda bayan nan kuma sai gashi a sabbin hotuna, yana fitowa daga mota, kuma yana takawa da kafarsa.

Daga baya-bayan nan ma, an ji rade radi na yamadidi na cewa wasu bata garin 'yan-siyasa, na kokarin hada kai da soji domin su hambarar da gwamnati domin su ci wasa kazamar riba ta siyasa, amma soji sun ce sun kame masu wasiwasin, sun kuma shawo kan lamarin.

Kwanaki kadan dai ya vrage wa gwamnatin ta Muhammadu Buhari ta cika shekaru biyu cif cif tun bayan karbar mulki daga jam'iyyar PDP, masu neman kujerarsa kuma na ganin lokaci yayi da zasu fara buga kugen siyasa domin gadonsa, a ciki da wajen jam'iyyar. Nan da shekara daya dai za'a fara zabukan cikin gida na fidda 'yan takara, ko shugaban zai iya takara? In kuma zayyi, shin zai sami goyon bayan jam'iyyarsa?

Wannan shine batun da masharhanta ke dubawa. Shi kuma ana yi masa fatan lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng