Amfanin shan rake ga lafiyar jiki

Amfanin shan rake ga lafiyar jiki

A baya mun kawo maku bayani a kan fa’idojin shan kankana, inda muka rahoto cewa shan kankana a lokacin da ake cin abinci ya na dakile amfanin ta.

Har ma muka ce idan har mutun zai sha kankana da zaran ya gama cin abinci maimakon tayi masa amfani, sai dai ma ta bige da illatasa, ta hanyar haifa masa matsaloli kamar irin su kumburin ciki, yawaita yin gyatsa da sauran abubuwa marasa dadi.

A yau kuma mun kawo maku sirrika dake tattare da rake.

KU KARANTA KUMA: Fa’idojin shan kankana da sanyin safiya

Amfanin shan rake ga lafiyar jiki
Amfanin shan rake ga lafiyar jiki

Legit.ng ta tattaro cewa shan rake na da matukar muhimmaci da kuma amfani a jikin dan Adam, inda muka kawo maku amfani guda 7 da rake ke yi a jikin dan Adam.

1. Yana taimaka wa koda wajen fitar fitsari yadda ya kamata.

2. Yana karfafa garkuwan Jiki, wajen taimakawa wajen kare cutar sanyi mura da

cutar daji.

3. Yana taimaka wa Hanta, Zuciya, Ciki, Ido, kwakwalwa da kuma al’aura.

4. Yana kara ruwan Jiki da karfi musamman ga masu aikin karfi ko aiki cikin rana.

5. Yana gyara fata.

6. Yana wanke hakora amma yana da kyau ka kuskure baki bayan kasha saboda kwayoyin cuta na iya samun zakin a matsayin abinci.

7. Gara ka sha Rake da ka sayi lemun kwalba don ya fi su amfani.

8. Yana maganin yunwa kuma baya da illa ga masu cutar ciwon sukari amma su kula karda su sha tayi yawa

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Har yanzu kana shan lemun kwalba?

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng