Kotu ta tasa keyar shugaban jam’iyyar PDP zuwa gidan yari

Kotu ta tasa keyar shugaban jam’iyyar PDP zuwa gidan yari

- Wata kotun Majistare da ke jihar Jigawa ta sa an tsareshugaban jam’iyyar PDP na jihar

- Ana zargin sa da wasu tsofaffin kwamishinoni na jihar da aikata wasu laifuka guda hudu

Wata kotun Majistare da ke garin Dutse babban birnin jihar Jigawa, ta sa an tsare shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party na jihar, Alhaji Salisu Mahmuda tare da wasu tsofaffin jigajigan gwamnatin jihar zuwa gidan kurkuku har zuwa ranar Talata, 23 ga wata Mayu domin yanke hukunci a kan bukatar bada belin su kamar yadda lawyoyi su ka nema.

Ana tuhumar Alhaji Salisu Mahmud tare da tsofaffin kwamishinoni guda biyar da jami’an kungiyar shugabannin ma’aikatan kananan hukumomi ta ALGON da aikata laifuffuka 4, amma sun musanta zargin da akeyi a kan su.

Wadanda lamarin ya shafa dai sun hada da shugaban jamiyyar PDP na jihar da wani Salisu Saleh Indirawa, da Nasiru Umar Roni, da Shehu Umar Chamo, da tsofaffin shugabannin kananan hukumomin Gagarawa Mukhtar Ibrahim Gongal, da na Kirikasamma Abba Mohammed Daguro.

KU KARANTA KUMA: Shugaban JIBWIS ya yaba da kiran gwamnatin Birtaniya, kan kokarin juyin mulki

Ana zargin su ne kan laifin cin amanar gwamnati, wanda hakan ya yi karo da sashe na 97 da 312 da 123 da kuma na 287 na dokar Final Code.

Yanzu haka dai alkalin kotun mai shari’a Usman Muhammed Lamin, ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Mayu na shekara ta 2017.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo da Legit.ng ta kawo na wani dan Najeriya da ya koka kan rashin madafa a kasar

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng