Mayakan Neja Delta Sun sace Dattijan Yankinsu.
- A Neja Delta, mayaka sun sace manyansu na kabilar Itsekiri, sunyi garkuwa sasu, kuma sun bukaci a biya su makudan kudi kafin su sako su.
- Sun kuma bukaci sai ma an saka su a jaddawalin kamfani mai hakar mai a yankin, a matsayin masu daukar albashi.
A jihar Delta mai arzikin man fetur, wata kungiya ta 'yan tada kayar baya, ta sace wasu dattijan yankin guda hudu, tayi garkuwa dasu, a yayin da tawagar manyan take rangadi tare da wani kamfanin hakar mai, a yankin, domin duba aikin gina asibiti da makaranta da kamfanin ke daukar nauyin yi domin amfanar garuruwan wajajen.
A tattaunawa da mayakan, domin daidaitawa wajen sako wadanda akayi garkuwar dasu, mayakan sun bukaci a biya su diyyar naira miliyan talatin, N30m, sannan a saka su a jaddawalin masu karbar albashi na kamfanin, da ma wasu karin bukatun.
KU KARANTA KUMA: Kotu ta tasa keyar shugaban jam’iyyar PDP zuwa gidan yari
A yanzu dai tattaunawa taci tura, jami'an tsaro sun baza kunnuwa don nemo maboyarsu da tarwatsa su, domin sako dattijan na yankin, dama wasu ma'aikatan kamfanin hakar man da abin ya rutsa dasu.
A wani ci gaba, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kungiyar Izala wato JIBWIS ya yaba da kiran gwamnatin Birtaniya, kan kokarin juyin Mulki.
KU KARANTA KUMA: Najeriya na cikin yanayi mai iya tarwatsewa – Obasanjo
An sami rahotanni da ke nuni da cewa wasu 'yan siyasa suna ingiza sojoji domin su tumbuke gwamnatin Shugaba Buhari, daga lokacin da shugaban ya tafi jinya, ya kuma ce bai san lokacin dawowarsa ba.
Shugaban sojin Najeriya Tukur Buratai, ya tsawatar da kada soji su kuskura su shiga sabgar siyasa.
Ku same mu a shafin:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Shin kin amincewa da Osinbajo a matsayin shugaban kasa a 2019 da dattawan Arewa suka yi yayi daidai?
Asali: Legit.ng