Kudin da Dangote ke samu a yini na iya biyan bukatan talaka a shekara

Kudin da Dangote ke samu a yini na iya biyan bukatan talaka a shekara

- Rahotanni sun kawo cewa rashin daidaito a kasar Najeriya ya bayyana tazarar dake tsakanin mawadata da talakawa da yadda wasu attajirai kalilan suka kankame tattalin arzikin kasar su kadai

- Hasashe sun nuna cewa mutane biyar da suka fi kowa wadata a Najeriya sun mallaki dukiyar da za ta iya raba al’ummar kasar gaba daya da talauci

- Mutumin da ya fi kowa arziki da wadata a Najeriya wanda shine Alhaji Aliko Dangote

Rahotanni sun kawo cewa rashin daidaito a kasar Najeriya ya bayyana tazarar dake tsakanin mawadata da talakawa da yadda wasu attajirai kalilan suka kankame tattalin arzikin kasar su kadai.

Rahotan da fitar da cewa mutane biyar da suka fi kowa wadata a Najeriya sun mallaki dukiyar da za ta iya raba al’ummar kasar gaba daya da talauci.

Wannan rahoto ya kuma gano cewa mutumin da ya fi kowa arziki da wadata a Najeriya wanda shine Alhaji Aliko Dangote wanda aka fi sani da mai kudin Afrika, yana samun kudin da ya ninka na talakan kasar sau 8,000 kuma kudin na iya biyan bukatun talakan na shekara daya.

Kudin da Dangote ke samu a yini na iya biyan bukatan talaka a shekara
Mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote

KU KARANTA KUMA: Kwanan nan Za a fara aikin layin dogo na Kano-Zaria-Kaduna

Mujallar Forbes da wasu cibiyoyi a tace tacen da suka yi a baya sun nuna cewa Alhaji Aliko Dangote ne ya fi kowa wadata ba kawai a Nijeriya ba, har ma a daukacin nahiyar Afirka.

Rahoton ya kuma ce fiye da mutane miliyan 112 na fama da talauci a Najeriya, amma attajiri mafi arziki a kasar zai dauki shekara 42 kafin ya kashe kudinsa, idan yana kashe dalar Amurka miliyan daya a kullum.

A wani ci gaba, Legit.ng ta rahoto cewa, a jiya ne Sarkin Zaria, Alh. Shehu Idris, ya karbi tawagar Shugaban hukumar harkokin safara ta jiragen kasa, a fadarsa dake birnin Zazzau.

Tawagar ta hada da Alhaji Usman Abubakar, Shugaban NRC na kasa, wanda ya tabbatar cewa, a kwanan nan ne za'a fara aikin sabon layin dogo na Zamani, wanda zai hade da hanyar jirgi da ta taho daga Abuja babban birni zuwa Kaduna garin Gwamna.

Digar jirgin zata tashi ne daga Kaduna, tabi ta ZAria, ta isa Kano. Shugaban, ya bada tabbacin cewa an samar da kudin aikin, an bada kwangilar ga kwararru daga kasashen waje. Zasu kuma iso da kayan aikinsu na zamani domin fara aikin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng