Fa’idojin shan kankana da sanyin safiya
- Ko kuna da labarin cewa shan kankana a lokacin da ake cin abinci ya na dakile amfanin ta?
- Lokaci ma fi inganci na shan kankana shi ne da sanyin safiya kafin mutun ya ci komai, sannan kuma a bari a kai akalla tsawon mintina 30
Idan har mutun zai sha kankana da zaran ya gama cin abinci maimakon tayi masa amfani, sai dai ma ta bige da illatasa, ta hanyar haifa masa matsaloli kamar irin su kumburin ciki, yawaita yin gyatsa da sauran abubuwa marasa dadi.
Lokaci ma fi inganci na shan kankana shi ne da sanyin safiya kafin mutun ya ci komai, sannan kuma a bari a kai akalla tsawon mintina 30,
Ko kuma da daddare a lokacin da abincin da aka ci na karshe ya gama bin jiki wato bayan ya narke a ciki.
Idan mutum zai jure ma aikata hakan to babu shakka zai ga banbanci, kama tun daga kan fatarsa zuwa karfi da kuma lafiyar jikin sa.
KU KARANTA KUMA: Turawa na taya Shugaba Buhari fatan samun sauki
Legit.ng ta tattaro maku fa’idojin da ke tattare da shan kankana da sanyin safiya ko kuma kafin a ci komai:
1. Gyara fatar jiki da magance ta daga kamuwa da matsalolin da zafin rana ke haifar wa.
2. Rage yiwuwar kamuwa da cutar daji da hawan jini da sauran su.
3. Inganta samun barci mai kyau.
4. Inganta karfin jiki da akalla kaso 23 cikin dari.
5. Kara saurin warkewar ciwuka da matsalolin fata da ninki uku.
6. Kara lafiyar ma’aurata wajen gudanar da ibadar aure. Sinadarin Arginine da ke cikin kankana na kara karfin maza kamar yadda magungunan kara karfi ke yi.
7. Inganta garkuwar jiki saboda kankana ta na dauke da sinadarin da ke shiga cikin jini ya wanke kwayoyin cutar da ke ciki.
An fi samun alfanun kankana idan aka shanye ta gaba daya har bawon ta da kwallayen ta, saboda su ma suna dauke da nasu sinadaran masu dumbin alfanu.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Har yanzu kana shan lemun kwalba?
Asali: Legit.ng