Mayakan Boko Haram sun fara komawa dajin Taraba

Mayakan Boko Haram sun fara komawa dajin Taraba

- Gwamnatin jihar Taraba ta koka kan yadda mayakan Boko Haram ke tururuwan samun mafaka a jihar ta

- Gwamnan jihar Darius Ishaku ne ya bayyana hakan ga Manjo Janar Adamu Abubakar, kwamnadan runduna ta 82 a Enugu a yayin da ya kai masa ziyara a jiya Alhamis a Jalingo

Gwamnan jahar Taraba, Darius Ishaku ya koka akan yadda mayakan Boko Haram da aka koro daga dajin Sambisa ke samun mafaka a dajin Suntai da ke jihar.

Ya bayyana haka ne ga Manjo Janar Adamu Abubakar, kwamnadan runduna ta 82 a Enugu a yayin da ya kai masa ziyara a jiya Alhamis a Jalingo.

Ya ce tun farko da aka fara samun kwararar mutane cikin jihar ya koka akan yiwuwar wannan matsala, amma sai aka zarge shi da kin baki, sai gashi yanzu suna fama da sakamakon.

Mayakan Boko Haram sun fara komawa dajin Taraba
Gwamnatin jihar Taraba ta koka akan yadda mayakan Boko Haram da aka koro daga dajin Sambisa ke samun mafaka a dajin Suntai da ke jihar

Ya ce yanzu haka mutane ba su iya tafiya akan hanyar Bali zuwa Suntai zuwa Takum ba tare da su na dardar ba.

KU KARANTA KUMA: Wasu abubuwa sun fashe a jami'ar Maiduguri

Ya nemi rundunar sojin Najeriya da ta kawo masu dauki domin a dakile ayyyukan mayakan, wanda ya ce har sun fara kashe-kashe, fyade da kuma sace mutane a jihar.

A wani al'amari makamncin wannan Legit.ng ta samu labarin cewa Wasu ‘yan kunar bakin wake na kungiyar Boko Haram sun kai hare-hare har sau biyu a jami’ar Maiduguri (UNIMAID) inda suka bar mai tsaron jami’ar da mummunan rauni.

Rahoto ya kawo cewa an kaddamar da harin ne a daren ranar Alhamis, 18 ga watan Mayu da kuma safiyar ranar Juma’a, 19 ga watan Mayu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin ya kamata shugaba Buhari ya mika wa mataimakin shugaban kasar Osinbajo mulki saboda kan al'amurran da suka shafi kiwon lafiyasa?

Asali: Legit.ng

Online view pixel