Mahaukaciyar guguwa ta lalata gidaje 1,000 ta kashe mutane 3 a Sokoto

Mahaukaciyar guguwa ta lalata gidaje 1,000 ta kashe mutane 3 a Sokoto

- Wata guguwa mai karfin gaske ta kashe mutum uku a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya.

- Jami'in Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa, NEMA,Suleiman Muhammed mai kula da jihohin Sokoto da Zamfara da Kebbi ne ya bayyana haka.

Ya ce lamarin ya auku ne ranar hudu ga watan Mayu na bana, inda guguwar ta ruguza gidaje fiye da gida 1,000 a kananan hukumomin Shagari da Tambuwal.

Legit.ng ta samu labarin cewa jimillar gidaje sama da 1,000 sun rushe a kananan hukumomin Anka da Maradun da Birnin Magaji. Daga watan karshen watan Afrilu na bana zuwa yanzu, guguwar ta shafi jihohin Kebbi, Sokoto da Zamfara.

"Idan annoba ta faru, da farko zamu je mu tabbatar da tsaro a gurin, kuma mu kididdige yawan barnar, sannan mu rubuta rahoton irin taimakon da suke bukata", in ji jami'in.

Guguwar ta haifar da asarar dukiya mai yawa.

Mahaukaciyar guguwa ta lalata gidaje 1,000 ta kashe mutane 3 a Sokoto
Mahaukaciyar guguwa ta lalata gidaje 1,000 ta kashe mutane 3 a Sokoto

KU KARANTA: Kaji yawan kudin da aka sace a Najeriya tun daga 1960

Suleiman Mohammed ya ce "Idan aka kiyasta abin da shafi Sokoto da Zamfara ya kai sama da miliyan 100 na Naira.''

Jami'in ya bayar da shawarar hanyoyin magance aikuwar irin wannan lamarin nan gaba, inda ya ce "Shuka itatuwa zai taimaka wajen rage asara irin wannan nan gaba".

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: