Kun san Magen da tafi ko wanne tsayi a duniya?
- Wani makeken mazuru a kasar Australia ya kafa tarihi inda ya zamo wanda yafi kowace mage tsayi a duniya
- Wannan mazuru ba shi da kuzari saboda girman jiki, amma yana da hikima sosai
Wani mazuru mallakin wata mata mai suna Stephy Hirst ya kafa tarihi ta hanyar zamowa mazurun da yafi kwanne mazuru tsayi a duniya, inda a yanzu tsawon magen ya kai mita goma sha biyu.
Sakamakon suna da wannan tafkeken muzuru ya yi a shafukan intanet, cibiyar kundin tarihin duniya ta tuntubi uwardakin mazurun, Hirst, inda cibiyar ta bukaci a aika mata da tsayin muzurun.
KU KARANTA: Gwamnati ta ware naira miliyan dubu 46 don ƙarasa aikin madatsar ruwa na Kashimbila
Dayake wannan mazuru dan gata ne, har shafin sada zumunta aka bude masa, kuma ya samu sakonni sama da 270,000 a mako biyu, kamar yadda rediyon BBC Hausa ta ruwaito
Tuni dai hotunan wannan muzuru suka watsu a jaridun kasar Australia da ma gidajen talabijin din kasar, Wannan an horar da shi, har yana iya bude kofofin gidan da kwabet din kitchen da na dakuna.
Da misalin karfe 5 na safe mazurun ke tashi daga barci, sai ya dan ci abinci kadan a matsayin karin kumallo, daga nan sai ya dan yi yawace-yawacensa, sai kuma ya ci danyen naman dabbar Kangaroo a matsayin abincin darensa.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mazurun ya kai nauyin kilogram 14, kuma ba shi da kuzarin yin aikace aikace ko guje guje kamar sauran maguna, asali ma saboda girmansa da da abin daukar kare ake daukar sa don kai shi wajen likitan dabbobi.
Mis Hirst ta ce, "Duk kawayenmu da abokamu naso su zo su ga muzurun." Ba su amince da hotunansa da nake sakawa a intanet ba, sun zaci hoton karya ne. Sai da suka ganshi a zahiri suka rika mamaki."
Uwardakin mazurun tace "Magen mu baya son yawo, ya fi so ya yi kwanciyarsa a akan gadon da yake kwantawa yana cin naman dabbar Kangaroo sannan kuma ya hana mu bacci da daddare,"
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kana ganin shugaba Buhari ya mika mulki ga Osinbajo?
Asali: Legit.ng