Shugabannin kasa da su ka fi kowa tsufa a Afrika (Ina matsayin Shugaba Buhari)
– A Nahiyar Afrika dai ana buga wani irin mulki
– Shugaban kasar Zimababwe Mugabe yana da shekaru fiye da 90
– Shugaban Najeriya Buhari kuwa ya fi shekara 73
Shugaba Muhammadu Buhari bai cikin shugabannin 10 da su ka fi tsufa a Afrika duk da kuwa ya zarce shekaru 70 a Duniya don kuwa akwai manyan sa.
1. Robert Mugabe
Shekarun shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe 93 a Duniya ke nan duk Afrika babu shugaban da ya kai sa tsufa da kuma dadewa a Ofis watau shekaru 40.
2. Beji Essebsi
Shugaban kasar na Tunisia ya haura shekaru 90 shi ma a Duniya wanda ya zo na biyu a jerin shugabannin da su ka sha miya.
3. Paul Biya
Shugaba Biya na nan Makwabtan Najeriya watau kasar Kamaru ya zarce shekara 83 a Duniya kuma har yanzu ana damawa da shi.
4. Abdelaziz Bouteflika
Shugaba Bouteflika na Algeria yana da shekaru 80 a Duniya kuma duk kasar Algeria babu shugaban kasar da ya kais a dadewa a mulki.
5. Ellen Johnson Sir-Leaf
Tana cikin shugabannin kasa mata da ake da su a Duniya, Shugaba Ellen Johnson ta Kasar Liberia tana da shekaru 78 a Duniya.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Yadda farashin kaya su ka canza bayan dawowar Buhari
Asali: Legit.ng