Jita-jitan juyin mulki: Buratai ya gargadi soji kan sa baki cikin Siyasa

Jita-jitan juyin mulki: Buratai ya gargadi soji kan sa baki cikin Siyasa

-Magana ta fito kan shirye-shiryen juyin mulki

-Tukur Buratai yayi gargadin kar-ta-kwana akan sojin kasa

Babban hafsan Sojin Najeriya, Laftanan janar Tukur Yusuf Buratai yayi gargadi ga hafsoshin sojin kasar da su kawar da hankulansu da bakunansu daga cikin siyasa ko kuma su dandana kudarsu.

Buratai ya baiwa Sojin masu sha'awar siyasa su tube kayan sarkin su.

Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Sani Kukasheka ne ya bayyana hakan a wasu alkakuman da ya saki ranan Talata bisa ga wata labarin da Buratai ya samu cewa wasu yan siyasa na ziyartan wasu hafsoshi kan wasu harkokin siyasa.

Jita-jitan juyin mulki: Buratai ya gargadi soji kan sa baki cikin Siyasa
Jita-jitan juyin mulki: Buratai ya gargadi soji kan sa baki cikin Siyasa

Saboda haka, babban hafsan Sojin kasar ya gargadi masu irin wannan tunani su shiga taiyayinsu.

“Duk hafsa ko sojan da aka kama yana shisshigi cikin al'amuran da bai kamata ba irin siyasa ya tuhumci kansa.

KU KARANTA: An rasa rayuka 20 a jihar Neja

Usman Kukasheka ya kara da cewa Buratai ya jaddada hukumar soji zata cigaba da biyayya ga kundin tsarin mulkin Najeriya.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng